ƘALUBALEN TAFIYATA DAGA KANO ZUWA ABUJA: Yadda tituna suka zama wajen Hada-hadar kuɗi.
Ko shakka babu, kowa zai yadda da ni cewa dokar zama wuri ɗaya (lockdown) a sakamakon cutar Kwaronabairus ta tada ƙura tuli wadda ta sa mutane ba sa iya ganin gabansu balle kuma sanin ina suka nufa a sakamakon hakan an samu ƙalubale masu yawa ta fuskar kasuwanci da rashin kewayawar kuɗi a hannun al’umma tare da ma rashin samun albashi ga masu aiki a kanfanoni da masana’antu da makarantun masu zaman kansu. Sannin kowa ne cewa gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna na sawun gaba-gaba wajen yaƙi da cutar da al’umma kansu har yau ke kokwanton ko ma akwai ta a gaske a garuruwansu ko dai ita ma cutar tana yin abin nan ne na “mutuwa ɗauki ran matsokaninki” saboda tana kama masu ziyare-ziyaren ƙasashen waje kaɗai da muƙarrabansu. Wannan ta sa wucewa ta Kaduna daga Kano zuwa Abuja tamkar tsallaka siraɗi ne mai ƙarfin tsarga zuciyar matafiya da damuwa. Wannan ta sa a yau nake son ba ku labarin irin ƙalubalen da na sha a wannan hanya ta Kano-Kaduna-Abuja tare da bayyana ra’ayina a kan wasu...