Posts

Showing posts with the label Hausa Poetry
Image
RAYUWAR TSUNTSUN NAJERIYA Ya Ilahi mahaliccin sararin samaniya, Wacce yau na ji tai shiru ba hauragiya. Na duba sararin sama ba tsuntsu ko guda, Na ɗan gusa sai na ga sheƙuna maƙil ana kokekeniya. Na ɗan matsa sai nai tambayar mujiya, Nan fa na firgita, na ga an cizge musu matashiya. Nai mamakin wane ne yai wannan cakwakiya, Sai sun ka gaya mini gwamnati ce tai kulleleniya. Ina dalili sai sun ka ce an samu mashasshara ne, Na ce wacce? Sun ka ce min ta Kwaroniya. Nai salati, nac ce to, wagga ad dalili na takunkumi? Sun ka ce shakka babu lamari har ya wuce na maleriya. Can dai na lura sun rame matuƙa ainun, Har ba ka iya bambance ɗan shila da masu kumariya. Nan sun ka ce rabon su da ƙoto tun watan jiya, Gwamnatin tai watsi da su ya ruɓaɓɓen naman miya. Sun ka ce  Anas tuna rayuwar tsuntsu mana, Na ce haƙƙun don sai ya fita kullum yake samun na abin miya. Sun ka ce ba damar fita daga sheƙa ko mutum ya sheƙa, Nac ce ina? Sun ka ce lahira don maharba na r...
MARYAMA DASSHIYA Da sunan Allah maƙagin halitta,         Mai rayawa mai kashe halitta, Salati ga Muhammadu ɗan gata,          Wanda ba shi fushi sai yawan kyauta, Alaye da sahabatiduk abin yabawa. Sun ce waqa ta Hausa bani iyawa,     Ni ko nac ce musu waƙa gare ni baiwa, Don cikin hikima ɗai taka tsaruwa,   Layuka zuwa ɗango sannan rerawa, Gashi ko yau sun yi tsit ba tankawa. Yaku zo waƙa ce za na yo ta,                Can cikin zuciya ne an ka tsara ta, Manufa dai yabo cikin soyayyarta,    Wacce ganinta ke sace nutsuwata, In zam fili da baɗili abin makancewa. Maryama kenan dasasshiya,               Ɗ aya tamkar uku babu jayayya, Kainuwa kike wane aikin kishiya,      Hasken silba, ki ɗau ido, ki ɗau zuciya, Farar  audug...