RAYUWAR TSUNTSUN NAJERIYA
Ya Ilahi mahaliccin sararin samaniya,
Wacce yau na ji tai shiru ba hauragiya.
Na duba sararin sama ba tsuntsu ko guda,
Na ɗan gusa sai na ga sheƙuna maƙil ana kokekeniya.
Na ɗan matsa sai nai tambayar mujiya,
Nan fa na firgita, na ga an cizge musu matashiya.
Nai mamakin wane ne yai wannan cakwakiya,
Sai sun ka gaya mini gwamnati ce tai kulleleniya.
Ina dalili sai sun ka ce an samu mashasshara ne,
Na ce wacce? Sun ka ce min ta Kwaroniya.
Nai salati, nac ce to, wagga ad dalili na takunkumi?
Sun ka ce shakka babu lamari har ya wuce na maleriya.
Can dai na lura sun rame matuƙa ainun,
Har ba ka iya bambance ɗan shila da masu kumariya.
Nan sun ka ce rabon su da ƙoto tun watan jiya,
Gwamnatin tai watsi da su ya ruɓaɓɓen naman miya.
Sun ka ce Anas tuna rayuwar tsuntsu mana,
Na ce haƙƙun don sai ya fita kullum yake samun na abin miya.
Sun ka ce ba damar fita daga sheƙa ko mutum ya sheƙa,
Nac ce ina? Sun ka ce lahira don maharba na rigegeniya.
Tas, tas, tatas, sun harba bindiga samaniya,
Sai ka ga gawa kwance ya mushen karyar jiya.
Ba ma wannan ba Anas ɗan tsaya ka ji,
Tsoffinmu na mutuwa asibiti babu magani ko kai magiya.
Ga shi ba damar kasuwa sai karɓar bugu,
An fifita su zabiya da ke mol-mol saboda cin hanceceniya.
Anas gaya wa gwamnati tai project na gina ƙaburbura,
Don cikin sheƙunan ga za mu sheka duka, sai ai bineneniya.
Anas ina ga batun palliatives na hatsin gwamnati,
Ko saboda biliyan sha biyar ba sauran taimakekeniya?
Don na ji wai babba da jaka ya wage babban riga,
Ka tuna masa don alƙiyama babu batun gwaggoniya.
Ina amfanin baɗi ba rai, tun da ibada ba mai yi?
Malamai sun zama zabi, sai a mazhabi sui ta rigegeniya.
Su ja aya da hadisai, wasu kuwa har kuɗi da muƙamai,
Ka ga ina za su faɗa aji tun da sun zama gaurakiya?
'Yan kasuwa mu zam tausayawa kuma abar riba,
Don ga jahimu wallahi sai an narka teɓa ta haramiya.
Talakawa matsalar gari, ku zagi shuwagabanni sarai,
Ku zo ga tsakaninku ba kyautayi sai ƙyashesheniya.
Sana'a ƙarama mu yi mun ƙi, duk jikinmu ya kwano,
Yai lambar talauci, ga tsatsar jahilci, ga karayar zuciya.
Kai ba ƙarfi ba, ba lambu ba, amma haihuwa ya ɓera,
Ka zubo kan titi kana Allah ba ya hana baki abin haɗiya.
Mu bar yara ba Ilimi don kuɗin na ɗa guda ne,
Ai haihuwar guzuma, shikenan al'umma sai roƙeƙeniya.
Mu za mu gyara don mu sam ƴanci ya mazan jiya,
Mu mori arziƙinmu gaba ɗaya har mu zarta Amurkiya.
Tamat nan zan ɗan tsaya, Ɗansalma ne ke wa'azaniya,
Ni dai aikina faɗin gaskiya, ko ku karɓa ko ku yi dariya…
Rubutawa;
©Anas Ɗansalma.
8/5/2020