Posts

Showing posts from July, 2020

#HIRARMU_A KAN SHA'ANIN HALIN DA IYAYE SUKE CIKI NE DA MALAMAI A GIDAJENSU A YAYIN WANNAN ZAMA NA KULLE.

Image
BARKAN MU DA SADUWA DA NI ANAS ƊANSALMA A WANI SHIRIN NA #HIRARMU. A WANNAN SATI HIRAR DAI A KAN SHA'ANIN HALIN DA IYAYE SUKE CIKI NE DA MALAMAI A GIDAJENSU A YAYIN WANNAN  ZAMA NA KULLE. Maƙociyarmu: Anas yauwa ku ne malaman makaranta. Don Allah wai yaushe za a koma makaranta ne gaba ɗaya. Na dai ji ana ƴan SS 3 da JS3 da Pri. 6 za su koma ko? Ni: Wlh haka da fari Boss Mustapha ya faɗa. Daga baya ya kuma abin ya bi ruwa. Sannan jiya nake jin ma ministan Ilimi yana cewa wai an fasa yin jarabawar WAEC da ma buɗe kowacce makaranta. Wlh har zuwa watan Agusta cewa yai kar a sa rai. Komawar nan fa, ina ga sai an tafi zuwa Disamba ko Sabuwar shekara ma. Maƙociyarmu: Anas na mutu! Amma an yi ɗan iska. In ce shi ma ministan Ilimin da akwai Boss a cikin sunansa ko? (Nai dariya ta ishe ni). Wlh tunda taƙamarsu Bosa-bosai ne ya kamata a samu Actor wanda zai kashe Boss ɗin nan kowa ya huta.  Ni: Kai! Wlh ba ruwa. Kisa fa kike faɗa! Maƙociyarmu: Dalla can ba kisan gaske ba. I...