#HIRARMU_A KAN SHA'ANIN HALIN DA IYAYE SUKE CIKI NE DA MALAMAI A GIDAJENSU A YAYIN WANNAN ZAMA NA KULLE.

BARKAN MU DA SADUWA DA NI ANAS ƊANSALMA A WANI SHIRIN NA #HIRARMU. A WANNAN SATI HIRAR DAI A KAN SHA'ANIN HALIN DA IYAYE SUKE CIKI NE DA MALAMAI A GIDAJENSU A YAYIN WANNAN  ZAMA NA KULLE.

Maƙociyarmu: Anas yauwa ku ne malaman makaranta. Don Allah wai yaushe za a koma makaranta ne gaba ɗaya. Na dai ji ana ƴan SS 3 da JS3 da Pri. 6 za su koma ko?
Ni: Wlh haka da fari Boss Mustapha ya faɗa. Daga baya ya kuma abin ya bi ruwa. Sannan jiya nake jin ma ministan Ilimi yana cewa wai an fasa yin jarabawar WAEC da ma buɗe kowacce makaranta. Wlh har zuwa watan Agusta cewa yai kar a sa rai. Komawar nan fa, ina ga sai an tafi zuwa Disamba ko Sabuwar shekara ma.

Maƙociyarmu: Anas na mutu! Amma an yi ɗan iska. In ce shi ma ministan Ilimin da akwai Boss a cikin sunansa ko? (Nai dariya ta ishe ni). Wlh tunda taƙamarsu Bosa-bosai ne ya kamata a samu Actor wanda zai kashe Boss ɗin nan kowa ya huta. 
Ni: Kai! Wlh ba ruwa. Kisa fa kike faɗa!
Maƙociyarmu: Dalla can ba kisan gaske ba. Ina irin na fim ɗin nan na Indiya. Ka ga da ana gamawa da su shikenan. 

Ni: Wannan Actor ɗin ai saidai in Baba Bahari ne, shi ne zai iya ɗaga musu red card.

Maƙociyarmu: Anas tashin hankalina yanzu rashin makarantar nan. Ashe dai malamai na taimakawa. Ka ga da da na tashi da sassafe na yi musu wanka da breakfast. Babbansu har taya ni yake yi, sai ka ga mai sauri. Suna gamawa ya wuce da su. Wallahi in samu in kwanta Anas na sha baccina na more. Wanke-wanke ma sai wajen 12 na rana nake wata ran. Sannan na ɗora girki. Suna dawowa by 3:00, sai sake ɗauraye su kawai da ruwa. By 4:00 sun wuce Islamiyya, sai Magariba ana kiran sallah za su dawo. Sannan kuma babansu ya dawo sai ya tashi inji ai kallo, ana yi, ana home work. Wanda zan iya na yi. Wata ran fakewa nake da girki naƙi yi musu ka san mun daɗe rabo mu da makaranta kuma Sakandiren ma fa Anas ta kwalliya muka yi (nai dariya). Yauwa ina gaya ma, wlh kafin 10 na gudu ɗaki ina baccina.

Ni:To ai yanzu hutawa ake kowa na gida.

Maƙociyarmu: Bala'i! To wallahi yanzu iya fitinar yaran nan sai da ta sa mijina ya siyo mana fanadol na roban nan. Bari-barin har ta ishe ni. Ni fa Anas da ana mai da ɗa ciki ko? Wlh da na mai da fitinannun ciki sai bayan Corona nan. Shi kuma da ya gaji, sai ya gudu wata majalisarsu a gidan Alh. Mustafa, ya kyale ni da fama. O ni 'yasu! Yanzu haka zan cigaba da wahalar nan har sabuwar shekara?

Ni: To ya za a yi. Ai malamai na ƙoƙari kuma a haka fa, su malaman private schools fa ko albashi ba a ba su saboda wai ba makaranta. Haka fa in mutum na da iyali zai zauna tangararau kamar emtin kwano. Kuma ba wani tallafi da gwamnatin tarayya ta ba su.

Maƙociyarmu: Allah sarki! Wlh har sun ban tausayi. Amma an yi shegun masu makarantu. Mutum ya gama wahalta muku cikin lokacin jin daɗi, sai da aka shiga tsanani za su yi watsi da su. Hmmm, tallafin gwamnati ko tallafin tallafa wa kai. A bakin rai-rai kamar karatun malam mai riya, amma ta mai riyan ma ta fi ƙarko don shi ana gani, a wurin Allah ne ba lada. Amma wannan kuwa, babu a ƙasa kuma a saman ma babu, sai ma zunubin haƙƙin al'umma. Kuma fa haka za a koma makaranta malaman da Allah ya sa suka rayu, su sake komawa ruwa?

Ni: Wallahi kuwa. Don ba aikin yin. Ina an ce mutum ya dogara da kansa. To, a ina zai samu jarin fara sana'ar. Banki kuma ina suka raina arziƙinka, ko kalla ba sa yi, domin sai ka kawo shidar wani abu na ƙimar kuɗin. Na gwamnati kuwa shi ne hotihon, don N-power ga shi nan majalisa na kashe mu raba da ma neman yin handamar kura. Allah dai ya ba su mafita kawai kin ji. Allah kawai zai biya malamin makaranta.

Maƙociyarmu: Wallahi kuwa. Allah ya saka musu kuma YA biya su da mafi girman lada. Amma fa akwai matsala don da ladan na ciyuwa ne kamar taliya, ai da sun zuƙulƙule shi ko sa yi kumari. Kalli dai malam Sa'idu kamar karar rake.

Ni: Wlh na gudu. Za ki fara ba'ar taki ko. Ga Saudat rigima nan dai ta fara kuka.
Maƙociyarmu: (ta ruga ɗaki da sauri) Na shiga uku! Wallahi rikici ta tashi!

Ni: Na ta fi ina tunanin to wai yaya ma za a yi da budget na Ministry of Education? Shikenan fa wataƙila ya sha ruwa shi ma Kwarona ta kama shi. Ko kuwa dai za su yi wa Buhari bayani ne cewa kuɗin nan ya ragu? Mtsss! Waye ma zai kula da wannan? Magun ma na EFCC da muke kallo a matsayin walakiri mai ƙoƙarin kama masu yi wa arziƙin ƙasa ta'annati, shi ma yanzu waje  kwana  goma yana komar walaƙiran fadar shugaban ƙasa. Wannan ƙasa, Allah ya shirya mu. Amma akwai matsala.

Rubutawa:
(c) Anas Ɗansalma.
10/7/2020

Popular posts from this blog

Every day humbles me

YADDA ZA KA YI AMFANI DA HARUFAN "ƙ da ɓ da ƴ ('y)" DOMIN YIN INGANTACCEN RUBUTU NA HAUSA A KWAMFUTA DA WAYAR HANNU