
AMFANI DA HARASAN ƘASASHEN ƘETARE: CIGABA KO NAƘASU GA AL’UMMAR AFIRKA DA NIJERIYA Da farko dai, wannan rubutu nawa ya samu tushe ne daga ƙarfin guiwar da na samu a rubutu ko jawabai na Prof. PLO Lamumba na ƙasar Kenya wanda yana ɗaya daga cikin tsirarun ‘yan gwagwarmayar ci da Afirka gaba (Pan-Afircanism) da suka rage da ke ƙoƙarin ganin an fidda A’I daga rogo. Wannan jawabi nasa, cikin wani salo na alamtarwa ya tsinka ni, sannan kuma ya miƙa kyakkyawan fata zuwa ga gwarazan magabatanmu ‘yan ƙishin ƙasar gaske. Abin ya yi matuƙar tsaya mini a cikin ƙahon zuci, musamman ta fuskar amfani da harasa na ƙetare wanda ya fi dugunzuma hankalina matuƙa gaya, ganin cewa mu sai yanzu muke shiri, shiri ma irin na baban-giwa. Harshe (language) wani abu ne na ni’ima da Allah ya yi wa ɗan‘adam kuma ya sanya bambance-bambance a tsakaninmu waɗanda suka haɗa da: wurin zamanmu (environment) da kuma tsarin yanayin tafiyar da rayuwarmu (culture) ta yau da kullum domin mu fahimci juna (to appreciate ...