Da sunan Allah maƙagin halitta, Mai rayawa mai kashe halitta,
Salati ga Muhammadu ɗan gata, Wanda ba shi fushi sai yawan kyauta,
Alaye da sahabatiduk
abin yabawa.
Sun ce waqa ta Hausa bani iyawa, Ni ko
nac ce musu waƙa gare ni baiwa,
Don cikin hikima ɗai taka tsaruwa, Layuka zuwa ɗango sannan rerawa,
Gashi ko yau sun yi
tsit ba tankawa.
Yaku zo waƙa ce za na yo ta, Can
cikin zuciya ne an ka tsara ta,
Manufa dai yabo cikin soyayyarta, Wacce ganinta ke sace nutsuwata,
In zam fili da baɗili
abin makancewa.
Maryama kenan dasasshiya, Ɗaya
tamkar uku babu jayayya,
Kainuwa kike wane aikin kishiya, Hasken silba,
ki ɗau ido, ki ɗau zuciya,
Farar auduga mai yawan
murmusawa.
Zo ka ga tsurar kyawu gun Indiyana, Fararan idonu ga hanci
miƙe Indiyana,
Cif-cif take gun fasali nata Indiyana, Ka ji zamani kowa dole ya yi ki Indiyana,
Sannan gare ki kallo
ne da sallamawa.
Ko cikin qur’ani akwai sunanki, Cikin
sutura kamila abinki,
Kowa shaida ne babu ruwan ki, Son
kowa, ana rububin ki,
Sai ta ce; “Anas, ni
kai nake yabawa”.
Layuka arba’in raunana suke, Cikin
baitoci takwas suke,
Saidai ba su iya misalta yaya kike, Kai ko numfashi da ke jikina ƙaƙa yake,
Duk tsawon zamanina
ba ki iya kwatantuwa.
Alhamdulillah ga ubangijin rayuka, Gani durƙushe a fadarka,
Wannan ta rahma
ga bayi duka, Roƙon alkhairi muke gare ka,
Allahu ka ba mu
soyayyar sanyayawa…….!
Rubutawa;
(c) Anas Ɗansalma