AMFANI
DA HARASAN ƘASASHEN ƘETARE: CIGABA KO NAƘASU GA AL’UMMAR AFIRKA DA NIJERIYA
Da
farko dai, wannan rubutu nawa ya samu tushe ne daga ƙarfin guiwar da na samu a rubutu
ko jawabai na Prof. PLO Lamumba na ƙasar Kenya wanda yana ɗaya daga cikin
tsirarun ‘yan gwagwarmayar ci da Afirka gaba (Pan-Afircanism) da suka rage da
ke ƙoƙarin ganin an fidda A’I daga rogo. Wannan jawabi nasa, cikin wani salo na
alamtarwa ya tsinka ni, sannan kuma ya miƙa kyakkyawan fata zuwa ga gwarazan magabatanmu
‘yan ƙishin ƙasar gaske. Abin ya yi matuƙar tsaya mini a cikin ƙahon zuci,
musamman ta fuskar amfani da harasa na ƙetare wanda ya fi dugunzuma hankalina
matuƙa gaya, ganin cewa mu sai yanzu muke shiri, shiri ma irin na baban-giwa.
Harshe
(language) wani abu ne na ni’ima da Allah ya yi wa ɗan‘adam kuma ya sanya
bambance-bambance a tsakaninmu waɗanda suka haɗa da: wurin zamanmu
(environment) da kuma tsarin yanayin tafiyar da rayuwarmu (culture) ta yau da
kullum domin mu fahimci juna (to appreciate ourselves) da kuma fayyace junanmu
(to identify ourselves). Waɗannan muhimman al’amura ne da ɗauke su cikin
al’umma, kowacce irin al’umma, tamkar karya ƙafafun mai ƙafa ne tare da musanya
masa su da na roba ko kuwa ace kai tsaye daidai yake da cire rai daga gangar
jikin ɗan’adam. Wannan ta sa Tuwaran yamma a lokacin mulkin mallaka ke ƙoƙarin
ganin sun musanya waɗancan abubuwa da su. Domin da zarar mutum ya rasa su, to
hatta dangane da tsarin tunaninsa yakan
canja.
Sakamakon
haka, Turawa ke ta ƙoƙarin ganin sun yaɗa harshensu da al’adunsu a tsakaninmu,
kuma hatta bayan sun ba mu abin da MU muka kira da “‘yancin kai” wanda a wajen
su “talala ne irin na ɗaure akuya da doguwar igiya,” sai ya cigaba da amfani da
dabaru kamar na kafa Ƙungiyoyi na Duniya a fannuka kamar na lafiya da uwa-uba
na kuɗi da tattalin arziƙi da ma sauran al’amura na yau-da-kullum. Wannan duk
dabara ce ta cigaba da bai wa waccen akuyar ta ɗaure abinci da kuma sanya ta
jin cewa a sake take, bayan a ɗaure take tamau.
Amfani
ko cuso mana harsunansu waɗanda tuni sun yi nasara tun a lokacin mulkin
mallaka. Taron Kasafta Ƙasashe na Afirka (Berlin Conference) da ya auku a 1885,
abu ne dai da tarihin Afirka ba zai manta da shi. Sannan hakan ya cigaba da
faruwa har zuwa yau a wata siga ta siyasa a ƙoƙarinsu na cigaba da gasa mana
ƙuma a hannu ko kuwa irin dukan nan na kura da shan bugu, gardi da kwashe kuɗi.
Sakamakon
haka, sai ya zamto Turawa sun yi wa ƙwaƙwalanmu wankin a wanki gara, ya zamto
mun mance cewa da arziƙinmu suka haɗa suka gina ƙasarsu, sannan muka saka wa
kawunanmu tunanin cewa mu ƙasƙantattu ne, ba ma su arziƙi ba, shi ya sa muka
kasa shiga a fafata da mu wajen inganta arziƙinmu, tare da barar kuɗi da
shuwagabanninmu ke yi daga wurinsu da sunan bashi. Inda irin waɗancan ƙuɗade ke
ƙarewa a aljihonsu da kuma asusun irin waɗancan ƙasashe da suke aron kuɗin daga
gare su. Hakan bai tsaya iya nan ba, domin hatta harshenmu ba ma tattalin
arziƙi ba yana neman ɓacewa ko kuwa in ce, yana shan muƙurar ɗaurin mage a
wuya. Domin baya ga Turanci, harsuna kamar Faransanci na kan gaba da yi mana
kutse. Inda a makarantu ake tilasta wa ɗalibai koyon sa da ma sauran
ire-irensa. Ba ina cewa koyon harsuna ba shi da amfani ba ne, domin ya tabbata
cikin tari tarihin Manzon Allah (S.A.W) cewa bayan ya yi hijira zuwa Madina, ai
yi ta samun aike na wasiƙu, musamman daga wajen Yahudawa (Jews) wanda Manzon
Allah ya kasance ba zai iya karanta su ba, don haka ya shawarci Zaid bin Thabit
da ya je ya koyi wannan harshe na Hibru (Hebrew language) don ya kasance
Musulmai sun guje wa sharrinsu. Inda Zaid, yake cewa: “na ko yi karatu da
rubuta harshen Hibru a kwana ko dare goma sha biyar, inda bayan haka na fara
karanta wasiƙu da Yahudawa ke aika wa Manzon Allah tare da rubuta musu amsa.”
Wannan ko shakka babu, abu ne da ke fito da muhimmancin koyon harshe. Saidai,
mu mun kasa fahimta da tantance manufa da ke sa mu koyon harshensu, sannan kuma
koyon harshen wani ai ba yana nufin watsi da naka ba ne, domin ai Zaid bin
Thabit bai yi watsi da larabci saboda kawai yana koyon harshen.
Abin
da ya fi shi ne, sai mu dawo da baya mu kalli tasirin yadda koyon irin waɗancan
harsuna ke haifar mana. Na farko dai, yana yin naƙasu ga harshenmu, don sai ka
ga yaro, ya kai saurayi ba zai iya rubutu ba da harshen da aka haifi iya da
kakanninsa ba, sai fa Turanci tsura. Na
biyu, koyon wasu harsunan na yin naƙasu ga al’adunmu, domin harshe da al’ada, ɗan
juma ne da ɗan jummai. Wannan ta sa da zarar ka ga yaro to burinsa ya yi rayuwa
irin ta Turawa, saboda yana ganin ita ce burgewa da cinyewa. Don irin shiga ta
banza da yawace-yawacen fati da fiknik na ɗaya daga cikin tasirin koyon harshe
da kwaikwaiyonsu da muke yi. Na uku,
koyon harsunan a irin tsarin da muke bi, yana lahanta mana tsarin ilimi,
a maimakon inganta shi. Ba buƙatar sake tabbatar mana da cewa, kaf a ƙasashen
da suka cigaba, ba ƙasar da ba da harshenta take amfani ba. Me yasa? Masani a ɓangaren
Ilimi da Ɗabi’a da Fasaha sun tabbatar da cewa, harshen uwa na da tasiri matuƙa
ga saurin fahimtar saƙo da ke cikin wani harshe daban. Domin a gina wannan
ƙwaƙwalwa ne da shi. Wannan ta sa da za ka ɗau ɗanka tun yana jariri ka kai shi
Turai da zai tashi da fahimtar harshen da ya fara ji kuma aka tashe shi da shi
ne.
Sakamakon
haka, nake ganin, a mayar da irin waɗannan harsuna wata hanya ta koyar da yaranmu
dabara ta amfani da su don yin bincike na ilimi da nazari, sannan kuma a
matsayin darasi ba hanya tsagwaro ta ba su ilimi ba. A maimakon haka, sai a
tilasta nazarin harsunanmu da kuma zama hanya ta isar da Ilimi a makarantunmu.
Bayan haka, ya kamata a ƙarfafawa masa a fannin fassara guiwa domin fassara
litttattafai da kalmomin fannu na fagagen Ilimi. Don ya zama komai namu ne.
Wannan zai kawo buƙasa da wadatuwar ilimi tare da sauƙi da saurin koyo da
koyarwa.
A
ƙarshe, ina kira ga iyaye (‘yan boko da ma’aikatan gwamnati) da ‘yan kasuwa da
hukumomin gwamnati da ƙungiyoyi sa-kai da su cigaba da jan hankalin al’umma da
wayar da yara da matasa kan rashin wayewa sun yi shakulatun ɓangaro da
harshensu. Domin muna da yawan da za mu iya mamaye duk wani harshe. Malamai a Jami’o’I
ma ya ya kamata su wayar da kan ɗalibansu wajen girmama harshensu. Mu sani cewa
kayan da ka ara, komai kyansu da ƙarkonsu ba za su taɓa dauwama ba wajen rufe
mana katari. Wata rana, mai ya yi zai ƙwace abinsa. Kukan kurciya, jawabi ne,
mai hankali ke ganewa. Na gode!
© Anas Ɗansalma.
31/2/2019.