YADDA ZA KA YI AMFANI DA HARUFAN "ƙ da ɓ da ƴ ('y)" DOMIN YIN INGANTACCEN RUBUTU NA HAUSA A KWAMFUTA DA WAYAR HANNU


SHIMFIƊA (Introduction)
Zan so farawa da tuna mana cewa harshen Hausa na kan cigaba da samun farin jini da zaurawa da ke ƙara zawarcin sa, inda toshinsu ya kai har ga ƙanƙamar sa da koyan sa da amfani da shi a harkoki na yau-da-kullum kama daga gida Nijeriya har zuwa ƙasar Sin waɗanda sun yi nisa tuni wajen yaɗa labarai cikin harshen na Hausa. Wannan ga duk mai hikima da fahimtar rayuwa ya san cigaba ne ga al'umma da ta mallaki wannan harshe.

Zai yi kyau mai karatu ya san cewa rubutun Hausa ba kawai bayyana ya yi ba daga sama, balle a rubuta shi kara-zube kamar yadda dubbun nan masu amfani da shi har ga cikin Hausawa kansu ke yi masa. Tarihin samuwar rubutun Hausa, idan aka ɗauke rubutun Ajami na Hausa, to na zamani ya faro ne da Turawa masu bincike (explorers) har zuwa ga Turawan mulkin da kuma dawowa hannun ƴan ƙasa, wato malumanmu na jiya da yau da suke a manyan makarantu da jami'o'i.
Tun a waɗancan lokuta Hausa ta riƙa gamuwa da ƙalubale, musamman na yadda za a yi amfani da waɗancan harufan (ɓ, ɗ, ƙ), inda Turawa kamar Bergery da J.F Schon da Hanns Vicher waɗanda suka yi amfani da kowanne ya kawo ta sa hanyar kan warware mas'alar. Wasu sun kawo batun ɗigo a ƙasa kamar na Ajamin Hausa, wasu kuma a riƙa saka karan-sama ('), amma sai wasu masana suka nuna amincewa a riƙa lanƙwasa samansu. Tun sannan aka warware wannan damuwa.

Saidai ta sake ɓullowa bayan samuwar wayoyin hannu da kwamfutoci kasancewar harufan na iya lanƙwasuwa ne a rubuce wanda a hakan ma ake jan daga tsakanin malamai da ɗalibai a makarantu, domin ba a ma maganar mutanen gari waɗanda ke cigaba da nuna halin ko-in-kula saboda taƙamar banza ta harshe na ne wanda a yanzu wasu al'ummomin kamar na Turawa da Sinawa, sai su ba wa mutum kashi a cikinsa. Baƙi ya fi ɗan gida kenan!
Farfesa Abdalla Uba Adamu, shugaban Jami'ar Koyo-daga-gida ta Nijeriya (Nigerian Open University) ya yi namiji ƙoƙari wajen ƙirƙirar wata manhajar kwamfuta mai suna "Rabiat" wacce ke sauƙaƙe amfanin da harufa masu lanƙwasa. An ci gajiyar wannan abu, saidai da yawa iya ɗaliban ilimi da malamai a jami'o'i ne suke amfanuwa da shi. Amma kafofin labarai kaf, In ka ɗauke Aminiya ta Daily Trust, babu wata jarida da ke damuwa wajen amfani da harufa masu lanƙwasar ciki kuwa har da BBC Hausa a yayin buga labaransu a rubuce.
Saidai, abin da al'umma da yawa ba su sani ba shi ne, nesa ta zo kusa dangane da wannan ƙalubale. Domin kuwa a kowacce kwamfuta yanzu akwai Harshen Hausa a cikinta (inbuilt) wanda abin da mutum zai yi shi ne kamar haka:

Mataki na farko, za ku shiga wurin nema ne (search) na kwamfutocinku,


sai ku nemo sashin gudanarwar kwamfuta (control panel),

 Sai ku shiga sashen agogo, harshe da yanki (clock, language and region),



sai ku danna harshe (language). Da shigar ku, za ku tarar da daɗa harshe (add language), inda dannawar mutum ke da wuya, jerin harsuna za su bayyana,





sai ku bi a hankali har ku kai kan harsuna da sunansa ya fara da "H" inda za ku ga Hausa + Latin, wato Hausa (Latin). Kuna dannawa sai ku duba ƙasa, inda za ku ga "add" sai ku danna shi.


 Shikenan kun kammala mataki na farko, sai ku fito gaba ɗaya kan filin fayau na kwamfutarku.

Mataki na biyu shi ne zuwa gefen dama na kwamfutarku, inda za ku ga alamomi na canjin batirinku da kwanan wata da sauransu. A nan za ku ga harufan ENG da ke nufin English, wato harshen da ke kan wayarki, English ne.
Sai ku ja kan kibiyar shiga sashe kansa tare da dannawa. Kuna dannawa zai fito za ku ga alamar HAU a ƙasan ENG ɗin nan. Sai ku danna HAU ɗin wanda ke nuna zaɓinku na harshen da kuke so kwamfutar ta zama "automatically," wato kai tsaye tana amfani da ita. Idan kuwa ba ka ga waɗannan harufan na "HAU" ba? To mataki na farko lallai bai yi ba yadda ya kamata.

Mataki na uku kuwa, shi ne a yayin da kuka shirya tsaf domin yin rubutu (typing) a MS-Word ɗinku. A madanin harufan kwamfutarku (keyboard), akwai madanni mai alamar "Alt" wanda guda biyu ne. Na hannun hagun shi ne "Alt," da na hannun dama "Alt Gr."


Don haka, za ku danna "Alt Gr" sannan ku danna ɗaya daga cikin harufa masu lanƙwasar da kuke son dannawa. Nan take zai fito shikenan.



SAUKE MANHAJAR HARUFA MASU LANƘWASA A WAYAR HANNU

Dangane da wayar hannu (smart phones), wayoyi da dama manya na zuwa kai tsaye da waɗannan harufa kamar Infinix hot 8 da sauransu. A irin waɗannan wayoyi, abin da mutum zai yi shi ne, idan yana don latsa harafin "ƙ" sai kawai ya danne "k" ɗin kaɗan, sai ya ɗaga. Zai ga "ƙ" ɗin ta fito. Mafi yawan mutane ba su san wayoyinsu na yin hakan ba.

Sa'annan, ga wayoyin da ba su da shi, akwai manhajoji da yawa na madannin rubutu waɗanda kan ba wa mutum damar shiga wani sashe a yayin da yake ƙoƙarin rubutu domin rubutu, inda zai duba sosai, inda daga ƙasa ko ma a saman gangar jikin madannan zai ga hoton ƙaramar taswirar duniya wanda daga nan mutum zai shiga domin ya daɗa harshen Hausa. Touchpal ɗaya ne daga cikin ire-iren waɗannan manhajoji da na daɗe ina amfani da su. Saidai kafin sauke manhajar, akwai buƙatar nutsuwa matuƙa. Yana da kyau mu yi haƙurin saukewa da kuma jure latse-latsen dannai domin yin rubutun Hausa ba tare da wata matsala ba.

SHAWARWARU:

1-Ga kafofin isar da labarai musamman na jaridu, kai da ma rediyo da talabijin da ke rubuta labaransu a shafukan sa da zumunta da don Allah su sani cewa kamar yadda ƴan boko kan ɗauki jarida ya karanta domin ƙaruwa da tataccen Ingilishi da gina rumbun kalmominsa (vocabulary development), haka ya kamata al'umma su same ku a jaridunku na Hausa. La'akari da tasirin labarai na intanet da kuma tasirin intanet ga rayuwar al'umma, sai nake ga cewa al'umma za ta yi saurin kwaikwaya da amfanuwa daga gare ku. Ina kuma kiran kan ku ƙara ɗaukar ma'aikata da suka karanta Hausa domin yin aiki editocinku domin samar da aiki mai inganci, musamman wajen amfani da harufan nan masu lanƙwasa.

2-Ga al'umma kuma, mu sani cewa an tasarma wata gaɓa da idan ba mu dage ba, to wallahi wasu mutane nan gaba su za su riƙa koyawa mana harshen. An ji ɓitir kenan. Sannan mu daure wajen amfani da harufan nan wanda yin haka zai sa mutane yin ta-ka-tsantsan tare da gyara wa juna a kodayaushe. Mu daure wajen nuna wa yaranmu muhimmancin sanin harshensu da al'adunsu. Ta haka, sai yara su fara fahimtar kunya da kawaici da juriya da girmama babba da haƙuri duk suna cikin ɗabi'un Hausawa kuma al'ada ce. Har'ila yau, mu tabbata suna Hausa a makarantunsu na boko, tun da ba za mu iya koya musu saboda ƙarancin lokaci ko rashin ƙwarewa, to mu tabbata suna yi. Mu tuna kowa ya bar gida, gida ya bar shi, kuma ɗan guntun gatarinka, ya fi sari ka ba ni.

Na gode.
Anas Ɗansalma
ɗansalma.blogspot.com
28/6/2020

Popular posts from this blog

Every day humbles me