Posts

#HIRARMU_A KAN SHA'ANIN HALIN DA IYAYE SUKE CIKI NE DA MALAMAI A GIDAJENSU A YAYIN WANNAN ZAMA NA KULLE.

Image
BARKAN MU DA SADUWA DA NI ANAS ƊANSALMA A WANI SHIRIN NA #HIRARMU. A WANNAN SATI HIRAR DAI A KAN SHA'ANIN HALIN DA IYAYE SUKE CIKI NE DA MALAMAI A GIDAJENSU A YAYIN WANNAN  ZAMA NA KULLE. Maƙociyarmu: Anas yauwa ku ne malaman makaranta. Don Allah wai yaushe za a koma makaranta ne gaba ɗaya. Na dai ji ana ƴan SS 3 da JS3 da Pri. 6 za su koma ko? Ni: Wlh haka da fari Boss Mustapha ya faɗa. Daga baya ya kuma abin ya bi ruwa. Sannan jiya nake jin ma ministan Ilimi yana cewa wai an fasa yin jarabawar WAEC da ma buɗe kowacce makaranta. Wlh har zuwa watan Agusta cewa yai kar a sa rai. Komawar nan fa, ina ga sai an tafi zuwa Disamba ko Sabuwar shekara ma. Maƙociyarmu: Anas na mutu! Amma an yi ɗan iska. In ce shi ma ministan Ilimin da akwai Boss a cikin sunansa ko? (Nai dariya ta ishe ni). Wlh tunda taƙamarsu Bosa-bosai ne ya kamata a samu Actor wanda zai kashe Boss ɗin nan kowa ya huta.  Ni: Kai! Wlh ba ruwa. Kisa fa kike faɗa! Maƙociyarmu: Dalla can ba kisan gaske ba. I...

I WILL BE YOUR WORSHIPPER

Image
The touch of your love Upon my harden heart Is like the touch of God Upon an unbeliever's heart When no one is expecting him To believe in the sanctity of your grace That I believe you're the most grandeur That have ever existed to me And much more worthy of my worship. Just know Bilkisu, Your heart will be a temple Where I shall always bow in devotion And with each day I will grow piety That you yourself will have to reward me With the paradise buried in your heart.

YADDA ZA KA YI AMFANI DA HARUFAN "ƙ da ɓ da ƴ ('y)" DOMIN YIN INGANTACCEN RUBUTU NA HAUSA A KWAMFUTA DA WAYAR HANNU

Image
SHIMFIƊA (Introduction) Zan so farawa da tuna mana cewa harshen Hausa na kan cigaba da samun farin jini da zaurawa da ke ƙara zawarcin sa, inda toshinsu ya kai har ga ƙanƙamar sa da koyan sa da amfani da shi a harkoki na yau-da-kullum kama daga gida Nijeriya har zuwa ƙasar Sin waɗanda sun yi nisa tuni wajen yaɗa labarai cikin harshen na Hausa. Wannan ga duk mai hikima da fahimtar rayuwa ya san cigaba ne ga al'umma da ta mallaki wannan harshe. Zai yi kyau mai karatu ya san cewa rubutun Hausa ba kawai bayyana ya yi ba daga sama, balle a rubuta shi kara-zube kamar yadda dubbun nan masu amfani da shi har ga cikin Hausawa kansu ke yi masa. Tarihin samuwar rubutun Hausa, idan aka ɗauke rubutun Ajami na Hausa, to na zamani ya faro ne da Turawa masu bincike (explorers) har zuwa ga Turawan mulkin da kuma dawowa hannun ƴan ƙasa, wato malumanmu na jiya da yau da suke a manyan makarantu da jami'o'i. Tun a waɗancan lokuta Hausa ta riƙa gamuwa da ƙalubale, musamman na yadda za a yi ...

A Letter To My Death Angel

Dear my death angel, Where have you been?               Come as much closer to me As you have always wanted to be. Dear my death angel, Don't you hear me groaning              For my loudest bleeding wounds Which are the story of misfortune? Dear my death angel, Don't you know I'm a wounded prey                Hunted by avaricious canines Who want to rip my flesh apart? Dear my death angel, Come to the North where I live                Forsake me not to the demons Whose bullets are more ruthless than you. Dear my death angel, My house is now a pool of blood                Brimming over my tattred head Filled with the fear of my marauders. Dear my death angel, Night is day and day is night                To me that I could see them ...

A BROKEN THUNDER

Image
Daam! Daam! Daam! It breaks, The sound of a broken thunder. Never do I ever heard of it before, But, now it’s the pulsation of my heartbeat. The thunder through the calm atmosphere, Came it as dark as Satan’s spiteful heart. Ratatatatah! Tastastastas! Ratatatatah! The sound of a heavy gun! The North is now a tatted garden asunder, Kidnapped I am day and night for ransom, That I've turned fountain for the vampires. Paralyzed we are with broken thunder, Driving us to untimely early graves, In numbers weakening our hands to bear. Ratatatatah! Tastastastas! Ratatatatah!                 The sound of a heavy gun! Fathers weep for their lovely pregnant wives, Mothers weeping for their innocent children, While children yell at corpses of their parents Everyone jittery and everywhere condolences, Which throw its stinging throes in our hearts As love kept reincarnating their bodily mirages Daam! Daam! Daam! It breaks, T...

RAPE: IS IT BECAUSE OF INDECENCY IN DRESSING OR IS A SELF-CENTRED CHEAP WAY TO DRIVE PLEASURE?

Image
I have seen how mistful torrents of pitiful posts and publications over the piteous raping cases that have filled the heaven hanging on newspapers, Facebook, and other social media platforms have been trending. I want to join hands in condemning this repulsive attitude. I have also read a myriad of views ranging from the female and male adults who have disappointingly condemned such acts. I was appalled by those who argue, mostly, from the female counterparts that indecent dressing by our young ladies which is accompanied with coquettish attitude is not a reason for why raping is becoming wild devouring the virginity of many innocent girls and babies. I won't say, with no pretentious male condescending and belittling reproach to the feminine gender that, despite being very innocent, their mode of dressing has been a strong wind that fans the men's (rapists) randiness. It is flimsy and characterless, even from atheistic or any form of a sense of reasoning, to think that n...

ƘALUBALEN TAFIYATA DAGA KANO ZUWA ABUJA: Yadda tituna suka zama wajen Hada-hadar kuɗi.

Ko shakka babu, kowa zai yadda da ni cewa dokar zama wuri ɗaya (lockdown) a sakamakon cutar Kwaronabairus ta tada ƙura tuli wadda ta sa mutane ba sa iya ganin gabansu balle kuma sanin ina suka nufa a sakamakon hakan an samu ƙalubale masu yawa ta fuskar kasuwanci da rashin kewayawar kuɗi a hannun al’umma tare da ma rashin samun albashi ga masu aiki a kanfanoni da masana’antu da makarantun masu zaman kansu. Sannin kowa ne cewa gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna na sawun gaba-gaba wajen yaƙi da cutar da al’umma kansu har yau ke kokwanton ko ma akwai ta a gaske a garuruwansu ko dai ita ma cutar tana yin abin nan ne na “mutuwa ɗauki ran matsokaninki” saboda tana kama masu ziyare-ziyaren ƙasashen waje kaɗai da muƙarrabansu. Wannan ta sa wucewa ta Kaduna daga Kano zuwa Abuja tamkar tsallaka siraɗi ne mai ƙarfin tsarga zuciyar matafiya da damuwa. Wannan ta sa a yau nake son ba ku labarin irin ƙalubalen da na sha a wannan hanya ta Kano-Kaduna-Abuja tare da bayyana ra’ayina a kan wasu...